Tsaftar Muhalli
kotu taci tarar ‘yan kasuwar Katako Naira dubu dari a Kano
Kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli ta yanke tarar Naira dubu ɗari ga shugabannin kasuwar yan katako da ke Na’ibawa a Jihar Kano.
Mai shari’a Auwal Yusuf shi ne ya yanke hukuncin, biyo bayan yadda kasuwar ta jibge shara ba tare da an kwashe ta ba na tsahon tsawon lokaci.
Da yake karin bayani jim kadan bayan yanke hukuncin, Kwamishinan muhalli na Jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso wanda mai rikon muƙamin babban sakataren ma’aikatar Dakta Garba Sale ya wakilta, ya bayyana yadda hukuncin ya kasance.
Dakta Garba Sale ya kuma ce, za su dauki matakin hukunci ga shugabannin tashar motar yan kaba saboda rashin tsafta.
Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano na gargadin mutane da su guji karya dokar fitowa gobe da safe da ake gudanar da duban muhalli na karshen wata.
Rahoton:Madina Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login