Connect with us

Kiwon Lafiya

Wata kungiya a Fagge ta mika wasikar kiranye ga shugaban majalisar dokoki

Published

on

Wata kungiya mai rajin ci gaban al’ummar Fagge mai suna Fagge Civil Society ta mika da wasika ga hukumar zabe ta kasa INEC wanda a ciki ta bukaci yin kiranye ga shugaban majalisar dokokin jihar Kano Yusuf Abdullahi Ata.

Wasikar wanda aka mikashi a jiya Talata ga shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Mahmud Yakubu a shalkwatar hukumar ta INEC da ke Abuja, ta bayyana cewa yin kiranyen ya yi daidai da sashe na 110 na kundin tsarin mulkin kasar nan.

Sakataren kungiyar Amar Sanusi Laure ne ya sanya hannu kan wasikar a madadin kungiyar.

Wasikar kungiyar ta kuma kunshi sanya hannun wasu al’ummar mazabar Fagge wadanda kungiyar ta ce suna daga cikin jama’ar mazabar da suka kada kuri’a ga dan majalisar wadanda kuma a yanzu suka yanke kauna da jagorancin da ya ke yi musu.

A wata wasikar kuma kungiyar ta zargi sakataren mulki na hukumar zabe ta kasa shiyyar Kano da kin bata hadin kai wajen mika musu wasu muhimman bayanai da kungiyar za ta yi amfani da su wajen gudanar da kiranyen.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,926 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!