Connect with us

Kiwon Lafiya

An samu dauke wuar lantarki a sassan kasarnan sakamakon lalacewar wasu na’urori

Published

on

An samu daukewar wutar lantarki a yankunan kasar nan da dama a daren jiya Talata sakamakon lalacewar wasu na’urori a tashoshin tunkudo wutar lantarki na kasar nan.

Rahotanni sun ce gobara ce ta tashi a bututun mai da ya taso daga Escravos zuwa Lagos wanda ya yi sanadiyyar lalacewar na’urori a kamfanin tunkudo wutar lantarki.

Lamarin dai ya yi sanadiyyar lalacewar bututu guda shida a kamfanin tunkudo wutar lantarki.

Da safiyar yau ne kuma ma’aikatar samar da wutar lantarki ayyuka da gidaje ta fitar da wata sanarwa wanda kuma ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar ma’aikatar lamarin ya yi sanadiyyar dakatar da aiki a tashoshin tunkudo wutar lantarki na Egbin da Olorunsogo da Omotosho da kuma Paras.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,434 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!