Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wata kungiya ta yi alkawarin tallafawa jihar Kano da ruwan sha

Published

on

Gamayyar wasu kungiyoyin kasa da kasa da ke rajin tallafawa dan Adam mai suna ‘Federation of the Associations that value Humanity’ dake da shalkwata a birnin Santanbul a kasar Turkiyya, ta sha alwashin ci gaba da gudanar da ayyukan samar da ruwan sha a sassa daban-daban na jihar Kano.

Babban jami’in kula da ayyuka na gamayyar kungiyoyin anan Kano, Askia Muhammad Nasiru Kabara ne ya bayyana haka, yayin tattaunawa da tashar Freedom Rediyo.

Ya ce gamayyar kungiyoyin suna duba bangarori da suka fi muhimmanci da kuma ke bukatar gudunmawar gaggawa.

Askia Muhammad Nasiru Kabara, ya kara dacewa, kungiyar tana kuma ciyar da marayu tare da daukar nauyin Karatunsu.

Wakilin mu Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito babban jami’in kula da ayyukan kungiyar anan Kano na kira ga masu hannu da shuni da su rungumi dabi’ar taimakon al’umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!