Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dokoki ta Kano ta nemi a’lumma su yi addu’o’in neman zaman lafiya

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci al’ummar musulmin kasar nan da su kasance masu addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaban kasa da kuma karuwar arziki a wannan lokaci da aka shiga sabuwar shekarar Musulunci.

Shugaban majalisar Alhaji Abdulazeez Gafasa ne ya bayyana hakan ta cikin sakon murnar shiga sabuwar shekarar musulunci da ya fitar fitr mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran majalisar, Alhaji Ali Bala Kofar-kudu.

Shugaban majalisar ya kuma yi addu’ar fatan dauki ubangiji sakamakon matsalar tattalin arziki da al’umma suka tsinci kansu a ciki sakamakon cutar COVID-19.

Alhaji Abdulazeez Garba Gafasa, ya kuma ja hankalin mutane da su kasance masu tsoron All… a al’amuran su na yau da kullum tare da rungumar zaman lafiya kamar yadda addinin Islama ya koyar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!