Labarai
Wata kungiyar APC ta bukaci Abdullahi Abbas ya gaggauta sauka daga mukamin sa kafin ranar biyar ga watan Yuli mai zuwa

Kungiyar APC Kadangaren Bakin Tulu ta bukaci shugaban Jam’iyyar a nan Kano Abdullahi Abbas da ya gaggauta sauka daga mukamin shugabancin Jam’iyyar kafin nan da ranar biyar ga watan Yuli mai kamawa.
Haka zalika kungiyar ta bukaci sabon shugaban Jam’iyyar na Kasa Bukar Dalori da ya sauke shugabancin na Abdullahi Abbas a nan Kano duba da rarraba kawunan yan jam’iyyar da ya yi.
Hakan na zuwa ne a wata ganawa da shugabancin kungiyar ya yi da manema labarai a yau ta bakin Sakataren kungiyar Kwamred Abubakar Abdullahi Dangarinnan.
You must be logged in to post a comment Login