Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An rantsar da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar APC a Kano

Published

on

Jam’iyyar APC ta kasa ta rantsar da zababben shugaban jam’iyyar na Kano Abdullahi Abbas.

An rantsar da Abdullahi Abbas ne a ranar litinin a Abuja jim kadan bayan mika shugabancin jam’iyyar na kasa a hannun gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello.

Sakataren yada labaran jam’iyyar na Kano Ahmad S Aruwa ne ya tabbbatar da hakan ga Freedom Radio.

 “A yanzu Abdullahi Abbas shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar mu a Kano babu wata sauran hamayya tun da ga shi shugabanci na kasa ya rantsar da shi “

Idan za a iya tunawa dai an yi tirjiya kan hallacin shugabancin jam’iyyar tsakanin tsagin gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsagin tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau lamarin da ya kai su da gurfana gaban Kotu.

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!