Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Wata Sabuwa: Ba wanda ya isa ya yi min riga-kafin Korona – Yahaya Bello

Published

on

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ce ba zai amince a yi masa allurar rigakafin cutar corona ba duk kuwa da cewa sauran takwarorinsa gwamnoni sun amince a yi musu a makon gobe.

Yahaya Bello ya bayyana hakan ne ta cikin shirin siyasa na gidan gidan talabijin na Channels a daren jiya juma’a.

Ya ce, shi kalau yake babu wata alamar cuta da ya ke dauke da ita, saboda haka babu dalili da zai sa ayi masa rigakafin cutar covid-19.

Haka zalika gwamnan ya ce ba zai bari ayi wa al’ummar jihar ta Kogi allurar rigakafin cutar ta covid-19 ba domin kuwa bai gamsu da ingancin allurar ba.

A cewar sa, jihar Kogi tana da matsaloli da dama da ke damunta, wanda cutar corona ba ta daya daga cikinsu, saboda haka su a gurinsu Corona ba wata matsala bace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!