Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Babu wani shugaban da yayi aiki irin nawa tun daga 1999 – Buhari

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce, babu wani shugaba a Najeriya da yayi aiki irin wanda yayi tun daga 1999 zuwa yanzu.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ta cikin jawabin da yayi wa ƴan ƙasa a yau, ta cikin sakon taya murnar cikia shekara 61 da samun ƴancin kai.

A cewar shugaban ya samar da ayyukan ci gaban ƙasa da tsarin zamantakewa mai kyau da shugabanci nagari ta yadda ƙasar ta zamo madubi a nahiyar Afrika.

Muhammadu Buhari ya ƙara da cewa, tun lokacin da ya karɓi mulki a hannun tsohohn shugaban ƙasa daga Goodluck Ebele Jonathan a 2015 Najeriya ta samu ci gaban da bata samu ba tun daga 1999 zuwa yanzu.

Ya kuma jaddada cewa tun lokacin da aka fara mulkin dimukradiyya a 1999 a zamanin mulkin sa ne kaɗai aka samu ci gaban da Najeriya ke buƙata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!