Labarai
WIDI JALO: Sama da Marayu 100 ne suka amfana da Tallafin kayan Sallah
Gidauniyar tallafawa mabukata da samar da ci gaban al’umma ta WIDI JALO, ta ce kamata ya yi a wannan lokaci da bikin Sallah ke karatowa kungiyoyin tallafawa al’umma da mawadata su mayar da hankali wajen sanya farin ciki a zukatan marayu da marasashi wajen samar musu da kayan da za su yi fitar Sallah.
Daya daga cikin membobin Gidauniyar ta WIDI JALO Hajiya Bilkisu Hamisu Mai Iyali ce ta bayyana hakan a lokacin da suke raba tallafin kayan sawa na Sallah ga Yara Marayu da mabukata a nan Kano.
Hajiya Bilkisu Hamisu Mai Iyali, a lokacin da ta ke raba kayan ta kuma ce a wannan karon sun raba sama da kaya guda 100 dinkakku na Maza da Mata domin sanya farin ciki a zukatan su musamman a lokacin bikin Sallah.
An dai raba kayan ne a yau Asabar 30 ga watan Maris na shekarar 2024.
Wasu daga cikin Iyayen yaran da yayan su suka amfana da talla sun bayyana jin dadin su, inda suka ce ” idan da Gidauniyar bata tallafawa yayan nasu ba basusan yadda za su yi ba a lokacin bikin na Sallah”.
Gidauniyar ta WIDI JALO ta ce za ta ci gaba da shiga lunguna da sakuna na jihar Kano da kauyuka domin tallafawa wadan da basu dashi.
You must be logged in to post a comment Login