Connect with us

Labarai

Wike ya gargadi ma’aikata kan bijirewa umarnin kotu

Published

on

Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya gargaɗi ma’aikatan birnin tarrayar da ke yajin aiki da cewa duk wanda ya bijirewa umarnin kotu ya ƙi komawa bakin aiki daga ranar Laraba, 28 ga Janairu, zai fuskanci ladabtarwa.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja, jim kaɗan bayan kotun warware matsalolin ƴan ƙwadago da ke birnin ta umarci ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin da suke yi.

Ya ce, “Daga gobe duk wanda bai koma aiki ba, za mu yi amfani da tsauraran matakai. Kuma daga gobe idan muka ga wani yana ƙoƙarin toshe ƙofa, za mu yi amfani da shi a matsayin misali. Dole ne doka ta yi aikinta.”

Ministan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta riga ta gana da ƙungiyoyin ƙwadago, inda aka tattauna dukkan ƙorafe-ƙorafensu amma hakan bai haifar da ɗa mai ido ba.

“Ina nufin idan ma’aikata sun gabatar da buƙatu 14, gwamnati ta magance 10 daga ciki, to mene ne kuma matsalar?” in ji Wike.

Ma’aikatan dai sun shiga yajin aikin ne tun daga makon da ya gabata inda suka buƙaci gwamnatin tarayya ta kyautata yanayin aikinsui da alawu-alawus din su.

Yajin aikin ya jawo tsaiko da rufe ayyuka a manyan ofisoshin gwamnati da dama a Abuja.

Biyo bayan hakan ne Wike ya shigar da ƙara a gaban koun warware matsalolin ƴan ƙwadago dangane da yajin aikin inda ta umarci ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!