Connect with us

Labarai

Badaru ya bada umarnin bude makarantun boko 40

Published

on

Gwamnan jihar Jigawa Mohammed Badaru Abubakar ya ce za’a bude makarantu 40 a jihar ya yin da bada umarnin dukkanin ma’aikatan jihar su koma bakin aiki daga rana 4 ga watan da muke ciki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ya yin da yake ganawa da manema labarai a birnin Dutse yana mai baiwa ma’aikatun ilimi da lafiya umarnin su fito da tsare-tsaren su wanda zai sanya kada a take dokokin cutar COVID- 19.

A dai kwanakin baya ne gwamnan ya bada umarnin ma’aikata dake mataki na 12 su koma bakin aiki.

A ranar 24 ga watan Maris ne gwamnatin jihar ta bada umarnin ma’aikatan su yi aiki daga gida don kare kan su daga cutar Corona.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!