Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Xavi Hernendez ya ci wasansa na farko a Barcelona

Published

on

Tsohon dan wasan kasar Spain Xavi Hernandez ya jagoranci Barcelona yin nasara a wasan farko a matsayin mai horarwa a wasan da sukai nasara da ci 1-0 a wasan hamayya na birnin Catalan a hannun Espanyol.

Wasan da ya gudana a ranar Asabar 20 ga Nuwambar shekarar 2021 a filin wasa Camp Nou.

Xavi ya samu nasarar wasan farko ne bayan dawowarshi a matsatin mai horarawa da hakan ya bashi damar samun maki uku.

Dan wasan kasar Holland
Memphis Depay ne ya zura kwallon a bugun daga kai sai mai tsaran gida.

Kawo yanzu Barcelona na mataki na 6 da maki 20 a wasanni 13 da ta buga.

Yanzu haka dai Xavi zai kuma jagoranci Barcelona fafatawa a gasar cin kofin zakarun turai Champions League da kungiyar Benfica.

Wasan da dole sai Barcelona ta samu maki uku domin kaiwa zuwa matakin kungiyoyi 16 na gasar ta 2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!