Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Har yanzu nine mai horar da ‘yan wasan Super Eagles – Gernot Rohr

Published

on

Mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Gernot Rohr, ya musanta labarin dake yawa cewa hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta koreshi.

Rohr ya ce har yanzu shine mai horar da ‘yan wasan na Super Eagles.

Sai dai Gernot Rohr dan asalin kasar Jamus, ya ce bayan da Super Eagles ta yi canjaras da kasar Cape Verde da ci 1-1 a wasan neman tikitin buga kofin Afrika da za a gudanar a kasar Qatar a shekara ta 2022, inda NFF ta bukaci da ya aje aikin horar da kungiyar.

Najeriya dai ta kare a matsayin ta 1 a rukunin da take na C, inda ta samu maki 13, hakan kuma ya bata damar buga wasan karshe na neman tikitin gasar.

Hakan kuma zai saka a fitar da kasashe 5 a Afrika da za su wakilci yankin.

Rohr mai shekaru 68 ya fara horar da ‘yan wasan Najeriya a shekarar 2016, inda kuma kwamtaragin sa zai kare a watan Dicambar shekarar 2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!