Labarai
Yaƙin Amurka da Iran ya dagula shirin Umrah na Musulman Najeriya

Rikicin yaƙi tsakanin Amurka da Iran ya janyo cikas ga tafiyar Umrah ta daruruwan Musulman Najeriya, bayan da kamfanonin jiragen sama suka soke tashin jirage zuwa Gabas ta Tsakiya. Lamarin ya sa mutane da dama da suka riga suka biya kuɗin biza, jirgi da masauki a Makka da Madina suka yi asarar miliyoyin naira.
Rahotanni sun nuna cewa wasu maniyyata sun shirya tashi daga Najeriya tsakanin ranar 4 zuwa 6 ga watan Maris, amma kamfanonin jiragen sama irin su Qatar Airways da Emirates sun dakatar da zirga-zirgar jirage saboda rufe wasu sararin samaniya a ƙasashen Gabas ta Tsakiya sakamakon hare-haren da aka yi a yankin.
Wasu daga cikin maniyyatan sun ce sun kashe sama da miliyoyin naira kan tafiyar Umrah tare da iyalansu, amma yanzu suna cikin damuwa domin kamfanonin jiragen sama sun ce za a iya sauya ranar tafiya ne kawai ba tare da dawo da cikakken kuɗi ba. Duk da haka, wasu da suka riga suka isa ƙasar Saudi Arabia sun ce ana gudanar da ibada lafiya, sai dai matsalar ta fi shafar zirga-zirgar jirage.
You must be logged in to post a comment Login