Connect with us

Labarai

Majalisa zata dakatar da jiragen saman Amurka da Burtaniya zuwa Najeriya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce daga mako mai kamawa zata dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga wasu kasashen duniya da suka hadar da Burtaniya da Amurka zuwa Najeriya sakamakon bazuwar cutar corona a kasashen karo na biyu.

Shugaban kwamitin kula da zirga-zirgar jiragen sama na majalisar dajjitai Smart Adeyemi ne ya bayyana hakan jiya a Abuja.

Adeyemi ya ce hukuncin dakatar da zirga-zirgar zai fara ne daga mako mai kamawa sakamakon yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar a kasashen, a don haka gwamnatin Najeriya zata sanar da matakin ta na gaba a mako mai kamawa.

Ya ce, ci gaba da shigowar baki daga kasashen zai kara yada cutar wanda a yanzu ana samun adadi mafi yawa na masu dauke da cutar a kullum.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Archives