Labarai
Ya kamata kasuwanni su tsabtace magudanan ruwan kafin damuna ta kankama- Ma’aikatar muhalli
- Yana da kyau su gyara magudanar ruwann don gujewa ambaliyar ruwan sama
- kuma yabawa kasuwar ‘yan Lemo bisa yadda suka tsaftace kasuwarsu
- A nasa bangaren shugaban kasuwar ta Yan Lemo ya ce tsaftace kasuwar ya zama wajibi a gare su
Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano, ta bukaci kasuwanni da su mayar da hankali wajen gyaran magudanan ruwansu da kuma kwashe shara sakamakon gabatowar damuna a bana.
Babban sakataren ma’aikatar Aliyu Yakubu Garko ne ya bukaci hakan a yau, bayan kammala duban tsaftar muhalli na karshen wata da aka gudanar a kasuwar Yan lemo da kuma tashar mota ta Na’ibawa.
Aliyu Yakubu Garko ya kuma yabawa kasuwar ta ‘yan Lemo bisa yadda suka tsaftace ta, sai dai ya bukace su da su yi biyayya ga gyare-gyaren da aka ba su a yayin ziyarar.
A nasa bangaren shugaban kasuwar ta Yan Lemo ya ce suna tsabtace kasuwar ne duba da mahimmancin tsabta, musamman ma su da suke siyar da kayan marmari, tsabtace kasuwar ya zama wajibi a garesu.
A gobe Asabar ne za a gudanar da duban tsaftar muhalli na karshen wata na duk gari a jihar Kano, a don haka ma’aikatar muhalli ta bukaci jama’a da su bata hadin kai don samun nasarar aikin.
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login