Connect with us

Manyan Labarai

Ya kamata Yan Najeriya su dakatar da zuwa asibiti kasashen waje-Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ‘’yan Najeriya a matsayin wadanda suka sha wahala sosai sakamakon cigaba da zuwa kasashen waje domin neman magani.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a Asibitin koyarwa na jamiar Alex Ekwueme ta gwamnatin tarayya dake Abakaliki lokacin kaddamar wa da mika kayan aiki ga hukumar Asibitin.

Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin ministan kimiyya da fasaha Dr Ogbonnaya Onu yace an kaddamar da ayyukan a Asibitin koyarwa na jamiar gwamnatin tarayya ta Alex Ekwueme ne domin magance matsalar zaizayar kasa.

Ogbonnaya Onu yace lokaci ya wuce da wani bangaren kasa za’a watsar da shi wajen gudanar da ayyuka sakamakon rashawa da ta yi katutu tsakanin al’ummar kasa .

Ministan na kimiyya da fasaha da ya wakilci Shugaba Buhari yace gwamnati ta damu kwarai da gaske game da lafiyar ‘’yan Najeriya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!