Connect with us

Manyan Labarai

Yansanda sun cafke wata mata da tura kishiyar ta rijiya a karamar hukumar Rano

Published

on

Wata kishiya a garin Rurum mai suna Hauwa Lawan yar shekaru 30 ta tura yar’uwarta kishiya Zuwaira Sani cikin rijiya da goyon da  mai suna Mustafa Sani dan shekara daya da rabi.

Yayin da rundunar Yansanda ta samu labarin ta kai dauki garin na Rururum inda suka tsamo ta zuwa asibiti daga nan ran Zuwaira Sani yayi halin sa.

Amma jaririn na ta dan shekara daya da rabi yana nan da rai.

A babban asibitin Rano ne dai Zuwaira Sani ta rasu.

Wacce ta aikata ta’asar Hauwa Lawan ta gudu

Mai maganin da yawun rundunar Yansanda ta Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan inda yace Kwamishinan yansanda na Jihar Kano CP Habu Sani ya bayar da umarnin a cafko Hauwwa duk inda take .

Da misalin karfe 1 da minti goma sha bakwai na dare ne Yansanda suka kamo Hauwa Lawan.

DSP Abdullahi Haruna yace kwamishinan yansanda na jihar Kano Habu Sani  ya bayar da umarnin akai korafin babban sashin bincike na kisan kai dake rundunar yansanda dake Bompai domin fadada bincike.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!