Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda ƴan ta’adda suka hallaka ɗan sanda a Kano

Published

on

Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun haura gidan wani ɗan sanda a nan Kano tare yi masa kisan gilla.

Lamarin ya faru ne a yankin Kureƙen-Sani dake ƙaramar hukumar Kumbotso inda mutanen suka haura gidan ɗan sandan mai suna Sajan Adamu Muhammad suka yi masa kisan gilla ta hanyar caka masa wuƙa.

Wani ɗan uwan marigayin da ya nemi a sakaye sunansa ya shaidawa Freedom Radio cewa a gaban matar marigayin da ƴarsa aka yi masa kisan gillar.

Marigayin dai yana cikin jami’an ƴan sandan dake aikin bayar da tsaro ga tawagar maimartaba Sarkin Bichi.

Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ƴan sandan Kano game da al’amarin sai dai har yanzu ba ta ce komai ba a kai.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!