Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

BUK ta musanta soke zangon karatun 2019/2020

Published

on

Hukumar gudanarwar jami’ar Bayero da ke nan Kano, ta musanta labarin da ake yaɗawa cewa ta soke zangon karatu na 2019/2020.

Jami’ar ta Bayero ta tabbatar wa Freedom radio cewa babu ƙamshin gaskiya game da batun sokewa ɗaliban zangon karatun na 2019/2020.

Daraktan yaɗa labaran jami’ar Malam Ahmad Shehu, ya ce ɗaliban jami’ar za su koma karatu a ranar 18 ga watan Janairun 2021.

A ranar Litinin ne wasu jaridun intanet suka riƙa yaɗa labarin cewa, jami’ar ta soke zangon karatun na 2019/2020.

Ci gaban labarin zai zo muku nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!