Sharhi
Yadda aka yi Najeriya ta samu Mulkin kai
A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960 ne Najeriya ta samu yancin kai daga kasar Burtaniya sakamakon yarjejeniyar tsarin mulkin da shugabannin siyasar Najeriya suka yi da turawan mulkin mallakar Najeriya.
Kafin a bawa kasar yanci akwai Gwamnonin mulkin mallaka da suka fito daga kasar Burtaniya tun daga lokacin da aka hade yankin arewacin Najeriya da na kudu a 1914.
Lokacin da Najeriya ke kokarin karbar mulki daga kasar Burtaniya an turo Gwamnoni bayan Lord Lugard wadanda suka fito da tsare tsaren da suka yi sanadin fara zabe a Najeriya.
Tsarin mulkin da ya fara kawo tanade tanaden zabe a Najeriya shi ne Hugh Clifford wanda aka fi sani da Clifford 1922 constitution
.Jamiyyar da yan Najeriya suka fara gwajin zabubbuka itace jamiyyar Nigerian National Democratic Party wato NNDP wacce Sir Herbert Heelas Samuel Macauly ke jagoranta , anyi zabe ,jamiyyarr ta NNDP ta shiga sannan tayi nasara a yankin Legas.
A shekarar 1953 danmajalisa na jamiyyar Action Group Chief Anthony Enahoro shi ne dan Najeriya na farko da ya fara kawo kuduri a gaban majalisar domin a bawa Najeriya yanci a shekarar ta 1953.
Amma wakilan arewacin Najeriya da suka fito daga jamiyyar mutanan arewa wato Northern People’s congress sun ki yadda da kudurin da dan jamiyyar AG Anthony Enahoro ya kawo na samun mulkin kai na Najeriya a shekarar 1953.
Tsarin mulkin da Oliver Littleton ya kawo na daya daga cikin tsare tsaren mulki da suka yi sanadin karbar mulkin Najeriya daga hannun turawan mulkin mallaka.
An rarraraba Najeriya zuwa shiyyoyi uku da suka hada da Arewa da yammacin Najeriya da kuma gabashi.
An kawo tsarin tarayya a shekarar 1954 aka raba kasar zuwa bangaran gabas da yamma da arewa.
Yankin gabas da yamma sun fara mulkar kansu a shekarun 1957 inda kuma yankin arewa ya samu na sa yancin a shekarar 1959.
A ranar 1 ga watan Oktoba ne wato yau shekaru 59 sarauniyar Ingila Elizabeth ta turo Princess Alexandra ta wakilce ta inda ta mika ragama ga Prime Ministan Najeriya na farko Sir Abubakar Tafawa Balewa .
Tsarin mulkin da Najeriya ta fara aiki da shi shine na Firaminista wanda kasar aka kwafo daga kasar Burtaniya, amma a shekarar 1966 ranar 15 ga watan Janairu wasu sojoji sun yi juyin mulki inda suka tumbuke Gwamnatin farar hula ta farko.
A zuwa yanzu yan Najeriya na ta kukan matsalar cigaba da kasar ke fuskanta a fannoni da dama da ya hada da tsaro da tattalin arziki.
A lokacin da kasar ta samu yanci ana da kimanin mutane da basu fi miliyan 40 ba amma a shekarun nan 59 ,Najeriya na da al’umma da suka kai kimanin miliyan dari biyu.
Koma baya a bangaren tattalin arziki da masanantu da kuma mutum miliyan 86 dake fuskantar matsanancin talauci kamar yadda kididdiga ta fitar.