Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda Buhari ya kaddamar da aikin shimfida layin dogo a Katsina

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aza harsashin aikin shinfida layin dogo a  Kwarin Tama da ke jihar Katsina a yau Talata.

Shugaban kasa Muhammadu ya bayyana hakan ta kafar Internet  wato visual ya yin da yake jawabin kaddamarwa.

Shugaba Buhari ya ce da zarar an kammala wannan aikin zai saukaka zurga-zurga da kuma sufuri musamman a Jamhuriyyar Nijar dake makwaftaka da Najeriya.

Sannan a cewar  shugaban kasar zai kasance hanyar samun kafar samar da kudaden shiga a tsakanin kasashen biyu da ma wasu kasashin.

Daga cikin wadanda suka halarci taron a Katsina sun hada da Gwamnan Maradi Zakari Ummar, Sai gwammanonin Kano da jigawa da Katsinan sannan sarakunan Kano, Katsina da Dutse da sauransu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kaddamar aikin shinfida layin dogo zai saukaka sufuri a tsakanin mutane.
Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!