Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda Buhari ya karbi bakuncin Sarkin Kano a fadar sa

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da yammacin jiya Talata a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Hakan na cikin wata sanarwa da Mai taimakawa shugaban kasar kan harkokin daukar hoto Mista Sunday Aghaeze ya fitar da yammacin jiya.

Rahotonni sun bayyana cewa har kawo yanzu ba a kai ga sanin batutuwan da shugaban kasar da kuma mai martaba Aminu Ado Bayero suka tattauna ba.

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa bayan hawan sa kan karagar sarautar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!