Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda dalibai suka ji da sanya ranar rubuta WAEC

Published

on

Da alama dai sanarwar sanya ranar rubuta jarrabawar WAEC ta zo wa dalibai a ba zata, duba da kwan gaba kwan baya, da aka rinka yi a baya, inda gwamnatin ta sanar da shirin komawa makaranta daga bisani kuma ta janye.
Kafin dai tafiya hutun dole sanadiyyar barkewar annobar cutar Corona, dalibai sun riga sun kammala rajistar WAEC abun da ya rage kawai shi ne sanya rana domin fara rubuta jarrabawar.
Freedom Radio ta ji ta bakin wasu dalibai da ke shirin rubuta jarrabawar ta WAEC wadanda suka bayyana mana farin cikin da suka yi da jin an sanya ranar rubuta jarrabawar.

Wata uwa a nan Kano Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya da muka zanta da ita, na ganin cewar, an rigaya an debewa dalibai karsashi daga jarrabawar ga kuma zaman gida na dole da aka shafe tsawon lokaci ana yi, don haka ta ce wannan lokaci da aka sanya ya yi kadan ga daliban domin su yi kyakykyawan shirin tunkarar jarrabawar.

Sai dai ga ‘yan gwgawarmayar rajin kare hakkin al’umma kuwa, cewa su ke ai abun farin ciki ne da godiya da gwamnati ta amince a rubuta jarrabawar, kamar yadda Kwamaret Bello Basi Fagge ya ce, wanda ya kara da cewa, gwamnati ta gaza wajen inganta ilimin daliban a lokacin da ake dokar cikin dokar kulle.

To amma a gefe guda masana a bangaren ilimi a kasar nan na cewar, sanya ranar rubuta jarrabawar a wannan takaitaccen lokaci abu ne da ko kadan bai dace ba, a cewar Dakta Munir Kamba, malami a sashen nazarin adana bayanai na tsangayar ilimi ta jami’ar Bayero dake nan Kano.

A kwanakin baya gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin cewa ta shirya tsaf, bayan da ta baiwa daliban jihar horo ta intanet, a don haka duk lokacin da aka sanya ranar fara jarrabawar ta WAEC to babu shakka daliban Kano za su kasance a mataki na gaba.
Kwamishinan ilimi na Kano Sanusi Sa’idu Kiru ne ya bayyana hakan cikin wata zantawa da ya yi da Freedom Radio a kwanakin baya.

Yayin da hukumomi ke ci gaba da duba yiwuwar sassauta zaman gida ga dalibai, a gefe guda dalibai da malaman islamiyya su ma na ci gaba da kira ga gwamnati kan ta amince su ci gaba da karatu, Malam Abdulkarim Salisu Malamin Islamiyya ne a nan Kano, ya roki gwamnati da ta sake yin duba na tsanake kan makarantun na islamiyya.
Tasirin annobar Corona dai ya yi illa ga bangarorin rayuwar al’umma da dama, wanda masana ke cewar zai yi wuya a iya maye gurbin tasgaron da ta haifar cikin kankanin lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!