Connect with us

Labarai

Yadda gobara ta kone dakin adana bayanan hukumar INEC

Published

on

Da safiyar Talatar nan ne wata gobara ta tashi a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ke nan Kano.

Gobarar wadda ta tashi da karfe goma na safe, ta kone sashen adana bayanai na hukumar tare da janyo asara mai tarin yawa.

Babban jami’in hukumar mai kula da shiyyar Kano Farfesa Riskuwa Arabu Shehu ne ya bayyanawa Freedom Radio cewa wata na’urar sanyaya daki ce ta fara kamawa da wuta a cikin dakin adana bayanai.

Riskuwa ya ce, duk wasu bayanai na hukumar da ke dakin adana bayan sun kone kurmus.

Tuni dai jami’an hukumar kashe gobara suka samu nasarar kashe wutar ba tare da rahoton asarar rai ko guda ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!