Connect with us

Labaran Wasanni

Yadda Gombe United ta yi ta’aziyya ga shugaban hukumar wasannin jihar

Published

on

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Gombe United, Dakta Larry Daniel , ya mika sakon ta’aziyyar tawagar, a madadin ‘yan ga shugaban hukumar wasanni ta jihar Gombe, Malam Hamza Adamu Soye,  bisa ga rasuwar dan sa, Adamu Hamza wanda ya rasu a Litinin bayan gajeriyar jinya a jihar Gombe.

Dakta Larry Daniel, yace rasuwar matashin mai shekaru 24 , abu ne mai ciwo matuka sai dai ya yi rokon shugaban da ya dau kaddarar rashin tare da nema masa afuwa.

Jami’in ya mika ta’aziyyar sa, ta kashin kansa bayan na tawagar ga dangin mamacin, tare da fatan Allah ya yafe masa.

Shugaban na Gombe United , ya kara dacewar tawagar tana tare da shugaban a cikin kowanne hali walau na farin ciki ko aka sin haka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!