Connect with us

Labaran Wasanni

Kwallon kafa: Montreal Impact ta dauki dan wasan Najeriya

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Montreal Impact dake a kasar Canada wadda Thierry Henry ke horaswa ta dauki dan wasan Najeriya Ibrahim Sunusi.

Sunusi dan wasan gaba mai shekara goma sha takwas ya saka wa kungiyar hannu a kwantiragin shekaru uku tare da kuma zabin karin shekara daya.

Daraktan wasannin kungiyar Olivier Renard, ya ce,”Kungiyar ta yi farin cikin daukar dan wasan duba da irin hazakarsa duk da cewa yana da karancin shekaru.”

Sunusi dai ya yi nasarar cin kwallaye goma a wasanni ashirin da biyu a gasar cin kofin kwararru ta Najeriya a kakar wasa ta 2018-2019 yayin da yake a kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United.

Yanzu haka dai Sunusi ya kasance dan Afrika na hudu a cikin tawagar Thierry Henry bayan Victor Wanyama dan kasar Kenya sai Mustafa Kizza daga Uganda sai kuma Clement Diop dan kasar Senegal.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!