Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda muka gano ministar da ta sayi kaddarar dala miliyan 37 a ɓoye– Abdurrasheed Bawa

Published

on

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Abdurrasheed Bawa, ya bayyana yadda ya ce, hukumar ta gano yadda wata minista ta sayi kadara a ɓoye da kudin-ta, ta kai dala miliyan talatin da bakwai da dubu ɗari biyar.

 

A cewar shugaban hukumar ta EFCC matar har ta ba da kuɗin kafin alƙalami da ya kai dala miliyan ashirin.

 

Sai dai Abdurrasheed Bawa  bai bayyana sunan ministar ko kuma bayyana karara cewa a wannan gwamnati ta rike mukamin ko kuma a gwamnatin baya ba.

 

Abdurrasheed Bawa ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da gidan talabijin na Channels, ta cikin shirin ‘Sunrise DAILY’.

 

Shugaban hukumar ta EFCC ya kuma ce, masu satar kuɗaɗen gwmanati suna amfani da ɓangaren sayan kaddarori ne wajen ɓoye kuɗaɗensu.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!