Labarai
Yadda Rundunar soja ta ceto mutane 642 a Katsina
Rundunar sojan ta kama barayin daji 220 tare da ceto mutane 642 a tsakanin watan Yuni da kuma Disambar Bara.
Mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar Birgediya Janar Benard Onyeuko,ya bayyana hakan a babban sansanin soji dake garin faskari na jihar Katsina.
Ya kuma ce sojojin sun kuma lalata sansanonin barayin dajin 197, baya ga gano tarun makamai kamar bindigogi da kuma Albarusai.
Haka kuma ya ce sojojin sun kama wadanda ake zargi da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba su 326 a shekarar da ta gabata.
You must be logged in to post a comment Login