Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shirin samar da ayyukan yi ga matasa zai rage talauci a Najeriya – Buhari

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce ta bullo da shirin baiwa Matasa aikin yi na wucin gadi wato Extended special public work program a kasar nan don rage talauci, da yunwa da rashin aikin yi da sauransu.

Ministan tsaron kasar nan janar Bashir Salihi Magashi ne ya bayyana hakan yau ya yin kaddamar da shirin a nan Kano.

Ministan ya ce “manufar gwamnatin tarayya shi ne ta hanzarta baiwa matasan  ‘yan Najeriya  su 774000 aikin da koyar da su sana’o’i  daga kananan hukumomi 774 na Najeriya”

A wani jawabi gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Nasir Yusif Gawuna ya yabawa gwamnatin tarayya bisa wannan kokarin ganin cewa mutane 1,000 a kowace karamar hukuma zasu ci gajiyar Shirin tare da naira dubu 20 har zuwa wata uku.

Wakiliya Zahrau Nasir ta  rawaito cewa hukumar samar da ayyuka ta kasa ce zata kula da yadda shirin zai rika gudana a kasar nan

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!