Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda ruwa ke kwanciya a hanyoyin Kano bayan tafka ruwan sama

Published

on

Jiya Alhamis an shafe kusan yini guda a nan Kano cikin yanayin ruwan sama, lamarin da ya jawo tsaiko wajen gudanar da wasu al’amuran jama’a, wannan dai shi ne karo na farko da aka tafka ruwa mai tsawo kamarsa a damunar bana.

Kwanciyar ruwan a yankuna daban-daban na Kano, abu ne da ya zamo ruwan dare wanda zai yi wuya ka kewaye manyan unguwannin kwaryar birnin Kano ba tare da ka ci karo da wuraren da ruwa ke taruwa ba, wanda wasu ke alakanta hakan da sakacin al’umma wajen gaza bada kulawa ta musamman ga magudanan ruwa, ko kuma barin wasu gine-gine ba da aka yi akan magudanan ruwa ba bisa ka’ida ba, a gefe guda ita ma al’umma na bada ta ta gudummuwar musamman wajen zuba shara a magudanan ruwa, da kuma rashin tsaftacce wasu magudanan ruwan.

Freedom Radio ta zagaya wasu daga cikin yankunan da wannan matsala tafi ta’azzara a kwaryar birnin Kano akwai Sabon Titin Dorayi, Titin Gidan Zoo, da kuma titin Zaria Road musamman daidai gadar Lado, a wani yanki na Unguwar Sani Mainagge da Unguwar Bubbugaje duka suna fuskantar wadannan matsaloli.

Wasu al’umma dake rayuwa a irin wadannan yankunan sun bayyana cewar suna cikin fargaba a duk lokacin da aka yi ruwan sama, yadda yankunan ke cika makil da ruwa.

Dr, Mustapha Zakariya Karkarna na tsangayar nazarin Muhalli a jami’ar Bayero, barin ruwa na taruwa akan hanyoyi na haifar da illoli da dama ga al’umma.

Haka abun yake a bangaren masana kiwon lafiya wadanda su ma ke cewar, baya ga illa ga muhalli wannan matsala na yin barazana ga lafiyar al’umma, kamar yadda Dr. Ibrahim Musa na asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano ya ce.

Haka kuma rundunar ‘yan sandan jihar ta ce tana yawan samun rahoton haduran da irin wannan cunkoson ruwan ke haifarwa, musamman yadda wasu matasa ke amfani da wannan damar wajen shiga ruwan da suka taru domin yin wanka, a don haka suke gargadin al’ummar Kano kan su kara kiyayewa a lokutan da aka yi ruwan sama, a cewar kakakin rundunar DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa.

Freedom Radio ta tuntubi kwamishinan muhalli na Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso don jin matsayar gwamnatin Kano game da wannan kalubale, wanda ya ce, gwamnatin tana yin iya kokarinta wajen ganin ta magance wannan matsalar kuma akan hakan ne ta fara yashe magudanan ruwan tun kafin saukar damuna.

Kwamishinan ya kuma nemi al’umma da su ci gaba da bai wa gwamnati hadin kai, wajen tsaftace muhalli domin kawo karshen wadannan matsaloli da kan gurbata muhalli.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!