Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda al’ummar Kano suka karbi karin farashin mai

Published

on

Bayan karin man Fetur da gwamnati ta yi, al’umma a nan Kano sun fara nuna damuwarsu bayan da wasu gidajen man suka fara sauya farashi, zuwa sabon farashi.

Mafi yawan al’ummar Kano da Freedom Radio ta zanta da su, sun ce ba su ji dadin wannan kari ba, Ahmad Usman daya ne daga cikin su, ya ce, “gaskiya wannan karin bai mana dadi ba, idan ba a yi sa’a ba yanzu sai ka ga kayan amfani yau da kullum sun tashi”.

Shugaban kungiyar dillalan man fetur ta kasa reshen jihar Kano, Alhaji Bashir Dan Malam ya ce, sun shirya bin karin da NNPC ta yi na mayar da man zuwa N150 daga N143 da ake sayarwa a baya.

A wayan Yunin da ya gabata ne, gwamnati ta mayar da farashin man daga N140 zuwa N143.

Sai dai masana tattalin arziki na cewar, wannan kari bai zo a lokacin da ya dace ba, kamar yadda Dakta Mukhtar Shehu Aliyu na sashen nazarin kasuwanci a jami’ar Bayero ya shaidawa Freedom Radio.

“Wannan ka ri bai dace ba, a wannan lokaci, duba da halin da al’umma ke ciki na farfadowa daga mashash-sharar tattalin arzikin da Corona ta kawo, kasuwanci har yanzu a sume yake, kuma wannan karin zai taimaka wajen tashin kayan masarufi”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!