Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kaduna-Abuja: Iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a jirgin kasa sun fito zanga-zanga

Published

on

Yadda iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja suka fito zanga-zanga

Iyalan wadanda masu garkuwa da mutane suka sace a jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna sun fara gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna da babban birnin tarayya Abuja.

Iyalan dainsun zargin cewa duk da garkuwa da yan uwansu fa aka yi, gwamnati ta yi shiru ba ta ce komai, duk da halin da yan uwan su ke ciki.

Har ma suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi duk mai yiwuwa wajen ceto musu yan uwansu.

Wasu daga cikin iyalan da aka yi garkuwa da yan uwansu

 

Iyalan dai na dauke da kwalaye masu rubutu da ke nuna bukatarsu ga hukumomi su shiga cikin lamarin.

Iyalan wadanda aka yi garkuwa da su kenan

Wannan dai ya biyo bayan wani gajeran bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna yadda masu garkuwa da mutanen ke azabtar da su.

Har ma a ciki suka sha alwashin ci gaba da azabtar da su har zuwa lokacin da gwamnati za ta waiwaye su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!