Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zanga-zanga: Za mu kawo karshen yajin aikin ASUU – Gwamna Ganduje

Published

on

Gwamna Ganduje lokacin da ya karbi tawagar masu zanga-zangar lumana

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta sanar da shirinta na yin duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ASUU.

Cikin shirin nata, da dauki gabarar bada shawarwari ga bangarorin biyu wato gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU.

Gwamna Kano Dakata Abdullahi Umar Gandije shi ne yayi wannan jawabi lokacin da tawagar masu zanga-zangar lumana ta yada zango a gidan gwamnatin.

A cewar Ganduje mu gamayyar gwamnonin Najeriya za mu tunkari gwamnatin tarayya da shawarwari domin ganin dalibai sun koma karatun su”.

Mun sani rashin biyan malamai albashi babbar matsala ce ga bangaren ilimi, don haka muna nan muna shiri don kawo karshen wadannan matsaloli” in ji Ganduje.

Wakilyar Freedom Radio Zahrau Nasir ta ruwaito cewa kungiyoyi daban daban ne suka halarci zanga-zangar lumanar wadda kungiyar kwadago ta shirya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!