ilimi
Yajin aiki: Ƙungiayar ɗalibai NANS ta buƙaci a kawo ƙarshen yajin aiki a ƙasar nan
Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa NANS ta buƙaci gwamnatin tarayya da ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU da su sanya buƙatun ɗalibai a gaba, wajen magance matsalolin tafiya yajin aikin da suke yi.
Shugaban ƙungiyar Sunday Asefon ne ya bayyana hakan da safiyar yau Litinin, ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce, yajin aikin da kungiyar ASUU ke shirin tafiya a kwanan nan, zai ƙara naƙasa harkokin ilimi.
Kungiyar ta ce, har yanzu ba a gama warware matsalolin da yajin aikin na bara ya haifar ba ga ɓangaren ilimi a ƙasar nan.
Idan za a iya tunawa tun a watan Disambar shekarar da ta gabata ne ƙungiyar ta ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe tsawon lokaci tana yi, sakamakon abin da ta zarga, na rashin biyan ta hakkokin ta da kuma rashin cika wasu alƙawura daga ɓangaren gwamnati.
You must be logged in to post a comment Login