Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Yajin aiki: Ƙungiayar ɗalibai NANS ta buƙaci a kawo ƙarshen yajin aiki a ƙasar nan

Published

on

Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa NANS ta buƙaci gwamnatin tarayya da ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU da su sanya buƙatun ɗalibai a gaba, wajen magance matsalolin tafiya yajin aikin da suke yi.

Shugaban ƙungiyar Sunday Asefon ne ya bayyana hakan da safiyar yau Litinin, ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce, yajin aikin da kungiyar ASUU ke shirin tafiya a kwanan nan, zai ƙara naƙasa harkokin ilimi.

Kungiyar ta ce, har yanzu ba a gama warware matsalolin da yajin aikin na bara ya haifar ba ga ɓangaren ilimi a ƙasar nan.

Idan za a iya tunawa tun a watan Disambar shekarar da ta gabata ne ƙungiyar ta ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe tsawon lokaci tana yi, sakamakon abin da ta zarga,  na rashin biyan ta hakkokin ta da kuma rashin cika wasu alƙawura daga ɓangaren gwamnati.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!