Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar likitoci reshen jihar Zamfara ta janye yajin aikin da ta tsunduma

Published

on

Kungiyar likitoci ta kasa NMA reshen jihar Zamfara ta janye yajin aikin mako guda da ta tsunduma sakamakon rashin biyansu kudadensu na albashi.

Shugaban kungiyar Dakta Mannir Bature ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a birnin Gusau jiya.

Sanarwar ta bayyana cewa, kungiyar ta janye yajin aikin ne biyo bayan amincewa da gwamannan jihar Bello Matawalle ya yi na biyansu kudadensu, adon haka suke umartar ‘ya’yan kungiyar da su koma bakin aikinsu.

Idan dai za a iya tunawa tunawa a ranar goma ga watan da muke ciki ne kungiyar ta umarci ‘ya’yanta da su tsunduma yajin aikin mako guda sakamakon rashin biyan su kudadensu da gwamnatin jihar tayi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!