Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yajin aiki: NARD Ku zo teburin sulhu don tattaunawa – Karamin ministan lafiya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bukaci kungiyar likitoci masu neman kwarewa da su dawo teburin sulhu don tattaunawa.

Karamin ministan lafiya Dr. Olorunnimbe Mamora ne ya bayyana hakan, lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Channels.

Ya ce, “Gwamnatin tarayya ba ta farin ciki da matakin da suka dauka na tsunduma yajin aiki, domin kuwa babban aikin su shi ne tabbatar da an bai wa mutane kulawa ta bangaren lafiya don kare rayuwar su”.

Idan za a iya tunawa tun a ranar 2 ga watan Agustan da muke ciki ne kungiyar likitoci masu neman kwarewa suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Sakamakon abinda suka zarga na rashin cika musu alkawuran su da gwamnatin ta yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!