Connect with us

Labaran Kano

Yan bindiga sun hallaka mutane a Kano

Published

on

Rundunar’yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun hari garin Bagwai dake nan Kano.

Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Kano DSP, Abdullahi Haruna Kiyawa , ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce suna cigaba da bincike.

Rahotonni sun ce maharan sun farwa garin da harbe-harben bindiga inda suka hallaka mutane tare da raunata wasu.

‘Yan bindigar sun shiga garin na Bagwai ne cikin mota da misalin karfe 10:30 na daren jiya Litinin.

‘Yan bindigar sun hallaka  wata ‘yar  gidan da suka kai harin wadda take  jigo a jam’iyyar PDP Hajiya Balaraba Sani.

Daga nan ne kuma suka harbe wani mutum mai suna Muhammad Sani.

Karin labarai:

Operation Puff-Adder sun farwa ‘yan bindiga dadin na Ansaru a dajin Koduru a Kaduna

‘Yan bindiga sun yi awan gaba da wasu tagwaye

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,751 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!