Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masu tseren doki sun hallaka wani matashi a Kano

Published

on

Wani matashi mai suna Shamsu Isma’il ya ransa sanadiyyar awon gaba da wasu masu tseren doki sukayi dashi a unguwar Kundila dake nan Kano.

Ana zargin gun-gun wasu matasa dake gudanar da tseren dawaki a yankin sun sukwane dawakai tare da awon gaba da al’umma da dama.

Baya ga Shamsu Isma’il da ya rasa ransa, masu tseren sunyi sanadiyar tsiyayewar ido guda daya na wani matashi mai suna Naziru Haruna.

Wani mazaunin unguwar ta Kundila mai suna Bilal Haruna kuma dan uwan daya daga cikin wadanda aka jikkata ya ce, ya na mamakin yadda masu hawan dawakin da ya kira da ‘yan kalen sarauta su ke cin karensu babu babbaka, kuma hukuma ta yi musu gum da bakinta.

A nasa bangaren Naziru Haruna da aka yi tsiyayewa ido guda daya ya shaidawa Freedom Radio cewa fatansa shi ne hukuma ta bi masa hakkinsa.

Mahrazu Isma’il shi ne, dan uwan marigayi Shamsu Isma’il da doki ya murkushe shi har ta kai ya rasa ransa ya ce, su talakawa ne, ba su da karfi sai na Allah amma ba za su yafe wannan kisan gan-gancin da aka yiwa dan uwan suba, don haka su ka mika maganar hannun ‘yan sandan ‘Yar akwa

Shima a nasa bangaren kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Freedom Radio afkuwar wannan al’amari kuma tuni sun fara daukar matakin da ya dace akai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!