Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan bindiga sun kai farmaki a garin Tiga

Published

on

A daren jiya Laraba 3 ga watan Maris 2021, wasu mutane dauke da makamai da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sunyi kokarin kutsa kai cikin gidan wani mutun a garin Tiga dake karamar hukumar Bebeji a nan Kano.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe daya na dare inda ‘yan bindigar suka yi kokarin kutsa kai cikin gidan mutumin mai suna Alhaji Rabi’u Tiga.

A cewar dan uwan Alhaji Rabi’u Tiga, Abdullahi Shehu, ya ce, “bayan zuwan ‘yan bindigar gidan sunyi ta faman harbin kofar da bindigoginsu don ta bude amma kofar bata bude ba kuma daga nan ne dan uwan nasa ya shaida masa abinda ke faruwa ta wayar tarho”.

“Bayan kofar taki budewa sai suka kama makocinsa Sulaiman domin ya nuna musu wata kofar da zasu iya shiga gidan amma yace bai sani ba sai sukai ta dukansa har sai daya suma, a yanzu haka yake kwance a Asibiti yana karbar magani”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!