Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya yi watsi da shawarar Sarkin Musulmi kan muƙabala

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da matsayar da Jama’atu Nasril Islam bisa jagorancin Sarkin Musulmi ta ɗauka kan shirin muƙabalar malamai a Kano.

Da yake zanta wa da Freedom Radio Kwamishinan al’amuran addini na Kano Dr. Muhammad Tahar Adamu Baba Impossible ya ce, basu samu saƙon Nasril Islam ba.

Ya ce, “Yadda kowa ya ke ji muma haka muka ji, kuma mu ba a ƙarƙashin ƙungiyar mu ke ba, wannan zama yana nan daram”.

Dangane da cewa zaman tuhuma za a yi ba Muƙabala ba, Baba Impossible ya ce, ba tuhuma ko husuma ce, ko kuma rigima aka kira ta sai an yi wannan zama.

Impossible ya ce, tuni shirye-shirye sun yi nisa lokaci kawai ake jira domin a fafata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!