Connect with us

Labarai

Yan bindiga sun kai wani hari yankuna da dama a Kebbi

Published

on

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai wani hari cikin dare  kan wasu yankuna  da dama a Jihar Kebbi, inda suka kone gidaje tare da janyo asarar rayuka da ba a bayyana adadin su ba.

 

 

Harin ya faru ne a daren Lahadin da ta gabata, lokacin da maharan dauke da makamai suka kai farmaki kan ƙauyuka da suka haɗa da Gebe, Kawara da Kalkami a ƙaramar hukumar Shanga.

 

Majiyoyin tsaro sun nuna cewa ana zargin maharan sun fito ne daga maboyarsu a dajin Wawa da ke Jihar Neja, wani yanki da aka daɗe ana danganta shi da ayyukan ’yan bindiga kuma yana kusa da wuraren da abin ya shafa. 

 

Da take tabbatar da faruwar lamarin rundunar ’yansandan Jihar Kebbi ta bayyana lamarin a matsayin harin hadin kai.

 

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Bashir Usman, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin kwantar da hankula.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!