Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan bindiga sun sace hakimi a Zamfara

Published

on

Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa a daren jiya Jumu’a, wasu ‘yan bindinga sun sace mutane 7, ciki har da wani hakimi a karamar hukumar Anka.

Wani ganau cikin mutanen garin ya shaida wa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba cewa bayan da maharan suka dauki mutanen sun kuma yi harbe-harbe a garin kafin daga bisani su tsere.

Wakilin namu ya tuntibi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar ta Zamfara SP. Shehu Muhammad amma bai daga wayarsa ba, kuma har kawo lokacin hada wannan labari bai samu ji daga gareshiba.

Jihar Zamfara dai na daga cikin jahohin dake fama da hare-haren ‘yan bindinga a Nigeria

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!