Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a fuskanci daukewar wutar lantarki a shiyyar Kano

Published

on

Kamfanin rarraba wutar lantarki shiyyar Kano Jigawa da Katsina ya ce za a sami daukewar wutar lantarki daga karfe goma na safiyar gobe Lahadi zuwa karfe uku na yamma sakamakon gyararrakin da zai yi.

Bayanin hakan na cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na kamfanin Ibrahim Sani Shawai ya fitar.

A cewar kamfanin gyararrakin da za a yiwa tashoshin zai bada damar kara karfin wutar da kamfanin tunkudo wutar lantarki na TCN ke aikowa babbar tashar wuta da ke Kumbotso.

A don haka kamfanin ya bukaci jihohin da lamarin ya shafa kan su bada hadin kai da goyon baya don ganin an kammala aikin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!