Labarai
‘Yan bindiga sun sace tsohon dan Majalisa

’Yan bindiga sun sace tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Ogun, Moruf Musa, a garin Ibiade da ke ƙaramar hukumar Ogun Waterside, a ranar Talata.
Moruf Musa, wanda ya taɓa rike muƙamin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Jihar Ogun daga shekarar 2007 zuwa 2011, an rawaito cewa an sace shi da misalin ƙarfe 7:00 na yamma, yayin da yake gudanar da sallar Magariba a masallacin da ke cikin gidansa.
Shugaban ƙaramar hukumar Ogun Waterside, Ganiyu Odunoiki, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa ’yan bindigar sun sace shi ne a lokacin sallar Magariba, inda suka harba bindiga a sararin samaniya yayin da suke tserewa da shi.
You must be logged in to post a comment Login