Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan boko-haram da ‘yan bindiga duk bakinsu daya – Gwamnan Ekiti

Published

on

Shugaban kungiyar gwamnonin kasar nan kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, ya ce, akwai alaka ta kut da kut tsakanin ‘yan Boko haram da kuma ‘yan bindiga da ke sace mutane suna garkuwa da su, a yankin arewa maso yamma da kuma kudu maso yammaci.

Ya ce gungun ‘yan ta’addar suna amfani da kudaden fansa da suke karba daga wajen jama’a suna sayan makamai don yaki da rundunar sojin kasar nan a yankin arewa maso gabas.

Gwamnan na Ekiti ya bayyana hakan ne jim kadan bayan wata ganawa da ya yi da shugaba Buhari a fadar Asorok.

A cewar gwamnan na Ekiti akwai kwararan hujjoji da ya ke alakanta ayyukan boko haram da na ‘yan bindiga da ke ta’asa a yankin arewa maso gabas.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!