Labarai
Yan fashin teku sun sace tare da garkuwa da masu fiton teku yan Turkiya
‘Yan fashin teku sun sace tare da yin garkuwa da wasu masu fiton teku ‘yan asalin kasar Turkiya a gabar ruwar kasar nan.
Kamfanin fiton tekun Kadioglu Denizcilik da ke kasar Turkiya, ya bayyana cewa, masu fashin tekun sun kai wa jirgin da masu fiton da ke ciki hari ne a kan hanyar su ta zuwa kasar Côte d’Ivoire bayan da suka fito daga kasar Kamaru .
Gidan talabijin na kasar Iran Press TV ya ruwaito cewa, jirgin kirar Paksoy yana tafiya ne ba tare da kaya mai yawa ba, bayan ya bar birnin Douala da ke kasar Kamaru zuwa birnin Abidjan.
Rahotanni na nuni da cewa, ba a samu raunata ko da mutum daya daga cikin mutanen da ke cikin jirgin ba, sai dai jami’an tsaro na ci gaba da kokarin ganin yadda za ceto su.
Ya ce ‘yan fashin tekun sun sace mutane goma ne bayan yiwa masu fiton tekun barazanar kashe su, inda sauran jami’an dake jirgin suka buya a wani sashe na jirgin.