Connect with us

Labaran Kano

‘Yan garkuwa sun sace dagaci a Kano

Published

on

Masarautar Karaye a jihar Kano ta bayyana cewa wasu masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa sun sace dagacin Karshi dake karamar hukumar Rogo Malam Ado Muhammad Lawan.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na masarautar Haruna Gunduwawa, ya fitar a yau Alhamis.

A rahoton da hakimin Rogo Wanban Karaye Alhaji Muhammad Muhammad Mahraz ya gabatar wa Sarkin Karaye Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II ya ce ‘yan garkuwar sun sace shi ne da misalin karfe 2:00 na daren Litinin din da ta gabata   13 ga wannan wata na Janairu.

Sanarwar ta kara da cewa, kimanin mutane 10 ne suka kutsa kai cikin gidan dagacin inda suka fito da shi tare da yin tafiyar kilo mita 10 sannan suka dora shi a kan babur.

Sai dai duk kokarin mutanen garin na kwatarsa ya ci tura sakamakon tarin manyan makaman da bat agarin ke dauke da su.

Tuni dai ‘yan garkuwar suka kira iyalan dagacin ta wayar tarho inda suka fara neman kudin fansa da har yanzu bas u bayyana adadinsu ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,910 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!